6 Oktoba 2021 - 12:56
Iran: Bai Kamata A Danganta Wata Kasa Ko Wani Addini Da Ta’addanci Ba

Mataimakiyar jakadan Iran a MDD ta yi watsi da danganta ta’addanci da wata kasa ko wani addini a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Zahra Ershadi ta na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda take gabatar da jawabi a gaban kwamiti na 6 a madadin kungiyar ‘yan ba ruwammu ta NAM.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ershadi ta kara da cewa bai kamata kasashen duniya su kasa bambanta kasa ko mutanen da suke gwagwarmaya don kwato kasarsu wacce aka mamaye da sauran ‘yan ta’adda ba.

Har’ila yau mataimakiyar jakadan ta yi allawadai da dukkan nau’o’in ta’addanci a duniya, musamman wadanda wasu manya-manyan kasashen duniya suke da hannu kai tsaye ko ta bayan fage wajen aiwatar da su.

A wani bangare na jawabinta Zahra Ershadi ta yi watsi da dukkan barazana da akewa kasashen duniya musamman ga kungiyar ‘yan ba ruwammu.

342/